Spread the love

Aysha Basheer tambuwal

Kayan ha]i

-farar shinkafa

-yis

-nono

-sukari 

-albasa idan ki na bu}ata


Yanda ake yin ta

 Da farko dai uwar gida za ki sami ]anyar shinkafa mai kyau da tsafta, ki ji}a ta a ruwa ta yi minti goma ko sha biyar ko rabin awa, sai ki wanke ta ki kai injin a marka]a miki, kuma kar ki bari a zuba ruwa cikin marka]en, idan shinkafar rabin mudu ce kisa yis cokali (1) kisa nono ka]an, sai ki buga ta sosai ki rufe, ki kai ta wurin zafi inda za tayi saurin tashi, idan ta tashi sai kisa gishiri da sukari daidai yanda kike son ]an]anon.

   Sai ki ]auko  dafaffiyar shinkafa ki zuba, ita ma yanda kike bu}atar ta a cikin }ullun masar ki, ana  yanka albasa in ki na so a ciki, sai ki koma bugawa ko juyawa ko motsawa sosai , sai ki ]ora tanda a kan wuta ki zuba mai, idan man yayi zafi sai ki dinga ]ebo }ullun a ludayi kina zubawa a tandar.

  Idan ki ka bar ~ari ]aya ya soyu sai ki juya ~ari ]ayan, idan ta soyu sai ki kwashe ki sa takarda   a akushi (food flask)  sai ki zuba masar a ciki kar ta huce, kafin ki gama suya sai ki rufe saman da takardar sannan kisa murfi ki rufe, haka za ki yi har ki kammala. Ana cin masar da miyar ganye ko miyar agushi, ko taushe ko romo irin wanda ke sa mai gida santi.

Amfanin Masa ko Waina a jikin Dan adam

   Masa kamar yadda aka sani abincin Bahaushe ne da ya gada kaka da kakanni, in da wasu ke gani ya samo abincin ne a wurin Larabawa a cudanyar sa da su a lokacin kasuwanci tun kafin kar~ar musulunci. Bayan ganin abincin a wurin su ya kar~a ya mayar da shi abincinsa, kamar sauran abincin da aka same shi ya na ci.

    Masana kiyon lafiya sun tabbatar da waina abinci ce, mai sanya kuzari kamar sauran dangin abinci irinsu tuwo shinkafa da masara ko rogo.

Sirrin Masa da sauran abincin Bahaushe ba ya da shi 

1. Masa ce ka]ai abincin da maza ba su yi komai gwanintar iya abincin su. 

2. Waina ko masa ita ce abincin da Bahaushe ya ]auka duk gidan da ka ganta ana ci akwai wadata a gidan.

3. Masa ce ka]ai ba a shakkun  baiwa kowa ita a ko’ina, domin ita ta na cikin jerin abincin Bahaushe na marmari. 

4. An camfata da cewa duk san da mutum ya ci masa ta sanya shi }uraje a jikin sa, to haka abun zai bi shi duk ya ci wainar  sai ya yi }urajen.

5. Kayan ha]in masa dukkan su dole ne a tanade su, wani baya isarwa wani sa~anin sauran abincin Hausawa.  

 6. Sukari da gishiri ba su ha]uwa wuri ]aya, amma masa ta kan adana su wuri ]aya tare da gamsar da mai ci. 

7.  Masa ce abincin na musamman da ya da]e }asar Hausa, amma ba kowace mace ke iya yinta ba.

8. Hausawa na girmama Waina fiye da sauran dangogin abinci, wanda hakan ya sanya duk bikin da ba su ganta ba, sukan ]auki bikin bai kammala ba a ~angaren abinci. 

9. Masa na cikin abincin da Bahaushe ke neman biyan bu}ata da ita, watau (sada}a). 

10. Masa na cikin abincin da Hausawa ba su wala}antawa, kuma ba su yin almubazzaranci da ita,  kan haka har camfin garga]i suka }ir}iro wa yara kanta “duk yaron da ya goge kashi da masa zai zama biri”.

Ma su karatu da fatan kun ilmantu da abin da ku ka karanta kan girkin Masa, in haka ne sai ku biyo ni wani lokacin don jin wani girkin Bahaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *