Spread the love

“Duk matar da mijinta ya yarda da ita, za ta shiga Aljannah.”

Mata wasu mutane ne a cikin al’umma da rayuwarsu ke tafiya cikin dambarwa da }o}arin samun tabbas a rayuwa.

Al-Madkhal ya ce wanda ya riga ya girmama ]an’uwansa da yake ganin yafi shi falala a cikin addini, wannan baya cikin babin fifitawa ga wani, domin  sa~ani nakan wanda ya bar fifitawar da babu makawa akwaita. To amma wanda ya bar ta zuwa ga abin da ke sama da ita, to, ba a so hakan ba.

Yarda da hukuncin Allah a kanka da }addarasa, da yi wa mutane mu’amala mai kyau don ka  ribanci bauatar Ubangijinka, da ri}a sauraron mutuwa a kowane numfashi, da yin abota da wanda zai nuna maka Allah a wajen tarayyarsa da maganarsa, ita ce rayuwar da mata yakamta su ri}e gam.

Akwai ha}}o}i guda goma sha ]aya da mata ke da su ga  mazajensu:

Na ]aya: Biyan sadaki, da yin walima abar so ce a aikata ta kan sunnah.

Na biyu: Daurewa kan cutarta da yin han}uri lokacin fushinta don koyi da Manzon Allah(S.A.W).

Na uku: Wasa da dariya da faranta rai

Na hudu: Yi mata ba’a gwargwado duk lokacin da aka ga abin }i ga shari’a a hana ta.

Na biyar: Tsakaitawa ga yin kishi don kar a yi mata mugun zato, ka da ka barta kara zube.

Na shida: Ciyar da ita abinci, shayar da ita abin da ka sha.

Na bakwai: Sanar da ita a}idar Sunnah da hukunce-hukunce addini.

Na takwas: Daidaita matan aure  a wajen kwana wajibi ne, kyautatawa mustahabi ce.

Na tara: Ladabtar da ita idan ta yi tawaye ta hanyar wa’azi da }aurace wa da duka ba mai cutarwa ba,  in ana tsammanin amfaninsa.

Na goma: Farincikin haihuwar da ta yi  namiji ko mace.

Na sha ]aya: Faranta ranta da kyauta idan bu}atar saki ta zo kuma kar ya watsa sirrinta.

Rayuwar mata bayan sun rasa mazajensu ta hanyar saki ko mutuwa ko tafiya ci rani, suna fama da kunci da matsin rayuwa.

Managarciya ta zan ta da wata mata(an sakaya sunan) ta ce “mijina ya sake ni da ‘ya’ya biyar mata uku maza biyu kuma yaran suka biyo ni gidanmu don ba wanda ya balaga cikinsu a haka Muke rayuwa a gidanmu tare da }annena uku maza da mahaifiyarmu kasancewar mahaifinmu ya rasu.”

“Ina fa]a maka mu tallakkawa ne a gidanmu kanena guda ne ke da zarafi fiye da kowa yana sana’ar gini waton mesin ne, to fa shi ne ke ]awainiya da mu, da kula da lafiyarmu, abin da ya samu shi ne namu, da iyalinsa saboda shi yana da mata daya da diya biyu mata.” A cewarta.

Ta cigaba da cewa “bari ka ji rayuwata bayan rabuwa da mijina duk yanda zan fada maka ina cikin kunci ba za ka fahimta ba yau shekara ta uku da fitowa gidan miji ban San na sanya sabo dinki ba, abincin da nake ci bana koshi sai dai na yi maganin yunwa, kuma mijin nawa baya aiko komi ga yaransa, in ka cire kayan sallah karama da yake ba su, ba wani abu da ke shiga tsakaninsu da shi, ba ruwanshi da ina suke kwana kan mi suke kwanciya, in sun tashi miye za su ci, karatu suke yi ko sana’a, shi anufinsa tun da ya rabu da mahaifiyarsu suma ya rabu da su, haka nake ta fama wani lokacin ma abin da za mu ci zai gagare ni, rayuwar ba da]i,” a cewarta.

Zubaida Muhammad mai shekara 27 da ]iya mace guda ta rabu da mijinta tun tana dauke da cikin ‘yarta ta ce “Na rabu da mijina tun ina da cikin yarinyar da muka haifa ya sake ni ne don mahaifiyarshi ba ta so na, bayan na haihu an ra]awa  yarinya suna to fa daga wannan lokaci ya jingine duk wani taimako da ]a ke bu}ata ga ubansa.”

“A sanda nake gidansa gwargwado yana kula ha}}i na ina ci da sha kuma ina samun sutura bayan mun rabu ne fa rayuwata ta shiga garari kasancewar gidanmu talakawa ne babana ya yi ritaya aikinsa fanshonsa bai fi dubu 10 ba, mamata ba ta wata sana’a a gida, ni ne babba a cikin yara takwas maza uku mata biyar da aka Haifa gidan.” In ji ta.

Ta ce “A gidanmu sai mu kasa dafa abincin da za mu ci, dana ga rayuwa na }ullemin na ro}i wani ma}wabcinmu da yake aikin kamfani ya samo min aiki a wurinsu na ko yi sa’a na samu aiki a matsayin sakatariyar wurinsu. Abinka da Bahaushe san da nake zama a gidanmu ba abinci ]iyata ba lafiya, }annena sun daina zuwa makaranta ba wani mutum da ya kawo mana ]auki amma dana fara fita aiki sai ka ga mutane na zuwa wurina da wajen mahaifina wai suna ba da shawarar na canja aiki don wanda nake yi a yanzu ba ya da kyau ana hul]a da maza, abin takaici wa]anda suka zo da wannan shawarar ba su kawomin wani aiki ba da zai canji wanda nake yi.”

“Wannan aikin dana samu shi ne ya taimakeni na dawo makaranta na gyara sakamakon  sikandare ]ina, na cigaba da ]aukar ]awainiyar abincin gidanmu da karatun ]iyata da kula da lafiyarta da tawa gaba ]aya. Rashin zaman gidan miji ba }aramar musiba ce  ga wadda ta saba, duk wahalar da take sha a gidan tafi sau}i ga wadda za ta tarar a waje, ina fatan sake samun miji na yi aure na koma rayuwar gaskiya da gaskiya.” A cewar Zubaida.

Atika Kabiru mai shekara 33 ta ce “Uwaye na sun aurar dani ga mijin da bana so, na kasa yin han}uri da shi har sai da muka rabu da shi, bayan mun rabu na gane kuskurena, rayuwar gidan miji ita ce mai inganci har dai in ka samu mai sonka wanda ya san girma da darajjar mace, ba wanda zai ri}a cin zarafinta ba wai shi tunanisa baiwa ce a wurinsa.”

“Har yanzu da nake a waje kuma nake son komawa gidan miji bana iya auren jahili a fannin addini da zamani, kuma ba zan auri wanda baya aiki ko sana’a ba, haka bana auren mashayi, da na fada gidajen masu wannan halin gara na koma ga Allah ban sake aure ba.

Hajiya Baraka Yusuf mai shekara 49 ta ce “Na rasa mijina ne a sanadin rasuwar da ya yi ban ta~a sanin ina cikin wata rayuwa ta rufin asiri ba sai da maigida na ya kwanta dama duk hidimar da yake yi mana da ta yaranmu ta koma kaina, na zama yanzu bana da wani lokacin hutu sai fa da dare, in yara sun yi kwana. Na kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali don bangon gida ya fa]i, wani lokaci nakan zauna in yi ta kuka kan abubuwa guda biyu na farko: rasa mai gidana domin sanda yake duniya bana komai daga ci sai barci. Na biyun kuma ina tuna wasu ‘yan uwana mata da suka rasa mazajensu musamman wa]anda suke talakawa ne, saboda ina kallon mu da aka barwa wani abu na juyawa yanda muke shan ba}ar wuya balle su da aka bari da yara ba komai, kai bari.”ta fa]i tana kuka.

Huraira Muhammad wadda mijinta ya barta ya tafi ci rani kusan shekara biyu bai dawo ba yakan yi mata aike can ba a rasa ba,ta nuna alhininta kan wannan abun in da take ganin gara a saki mace da aje ta, saman wannan turba ta wahala. ‘mace ta san mijin aure ta rasa yafiye mata alheri da ace tana jiransa ne ya tafi ci rani’ fahimtar ta kenan.       

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *