Spread the love

1. ME NE NE LAYYA?Layya itace yanka daya daga cikin dabbobi ni’ima wadanda Allahu {SWA} ya arzuta mu da su. Kamar yadda yazo a cikin Kur’ani,”Lallai mu mun ba ka kyauta maiyawa. Ka yi Sallah zuwa ga Ubangijinka, ka yi yanka [Surat Kausar 1&2]. Haka kuma wata ayar tana cewa, “Rakuma mun sanya su daga cikin ibadoji na Allah a gare ku alheri ne”{surat Hajji 36}. Haka kuma a cikin suratul An’am aya ta 162 in da aka ce ma Annabi lbrahlm,”Ka ce lallal Sallata da Yankana da Rayuwata duka ga Allah {SWA} suke. 2. WA NE NE YAKE YIN LAYYA?Layya Sunnah ce ta Manzo {SAW} kuma Sunnah ce mai karfi a kan kowane Musulmi babba ko yaro, namiji ko mace, mazaunin gida ko matafiyi, wanda ke da wadatar da idan ya yi layyar ba zai kuntata wa kansa ba.Saboda hadisin Abu Huraira wanda Imam Ahmad ya fitar da shi ya ce, Manzo{SAW) ya’ ce wanda ke da wadata baiyi Layya ba kada yazo Masallacinmu”.3. DA WACE IRIN DABBA AKE YIN LAYYA?Ana Layya da rago ko tunkiya, dan-akuya ko akuya, sa ko sanuwa, rakumi ko rakuma. Wannan kuwa saboda Hadisin Aisha (RA) ta ce, Manzo {SAW}ya yi umurni da raguna guda biyu masu kahoni, masu takawa cikin baki. masu durkushi cikin baki, masu kallo cikin baki. Aka kawo masa su domin ya yi Layya da su ya ce mata ya Aisha, kawo mani wuka ki wasa ta da dutse, sannan ya amshe ta ya kada ragunan ya yanka su, sannan ya ce, Bismillahi ya Allah ka karba daga Muhammadu da lyalan Muhammadu de Al’ummar Muhammadu .Sannan ya yanka. Wanda bai samu irin wannan ba sai ya yi Iayya da wanda ya samu.4. CIKlN WANNAN DABBOBIN WANENE YA Fl?Wanda ya fi shi ne irin wanda Manzo{SAW)Ya yi Layya da shi kamar yadda ya zo a sama. Rago mai kahoni, mai gabansa duka kansa da kafafuwansa baki, dayansa fari watau mai gaban hankaka.5. YAUSHE NE AKE YANKA DABBAR LAYYA?Ana yanka Layya ne da hantsi bayan an sauko Idi kuma Liman ko Sarki ya yanka tasa Layyar. Saboda Hadisin Abu Burdata {RA}ya ce, Na yanka Layya kafin Sallar Idi sai Manzo (SAW) ya ce mani akuyarka akuyar nama ce,. sai na ce ya Manzo Allah ina da wata yar akuya amma fa Jaza’a ce, watau karamar yar’akuya mai watanni da ba su kai shekara guda ba, ya ce ka yanka ta amma ba a yarda ma kowa ba banda kai. Sannan ya ce, wanda ya yanka kafin Sallar Idi kansa ya yanka mawa.Wanda ya yanka bayan Sallah ‘to yankansa ya cika kuma ya dace da Sunnah ta Musulmi. (Buharl da Musulim suka fitar da shi}. Haka kuma an samu a yi ta yanka dabbobin Layya har bayan rana ta yi zawali watau ta gota daga tsakiya, daga nan an so a kame daga yanka kuma sai gobe da hantsi.  Wannan hadisi na nuna maka cewa Wanda ya yi yanka kafin Sallar ldi ba ya da ladar Layya sai dai aci nama kawai.Haka kuma baa yarda a yanka akuya wadda bata kai shekara guda ba ta shiga cikin ta biyu.6. KWANAKI NAWA NE AKE LAYYA CIKIN SU?Ana Layya ne cikin kwana uku na Zulhajjih sune 10, 11 da12 ga wata, sai dai mafifici shine ranar Sallah watau ranar 10 ga wata. 11 da 12 kuwa watau kwana daya ko kwana biyu. bayan Sallah sai in da laluri. 7. DA SHEKARA NAWA NE WADANNAN DABBOBIN SUKE ISA LAYYA?Wadannan dabbobin suna isa Layya ne in sun kai shekaru kamar haka. Saboda hadisin Jabir ya ce, Manzo{SAW} ya ce, kada ku yanka dabba sai mai shekaru, idan ya tsananta gareku ku yanka Jaz‘a watau tinkiya wadda bata kai shekara ba. ldan muka kalli wannan hadisi me ne ne Jaz’a a cikin dabbobi kuma wane shekaru ne hadisin yake nufi, malamai sun yi sabani akan wannan. Jaz’a daga cikin tumaki wadda ta cika wata (6) wannan shi ne Mazhabar Hanafiyya da Hanbaliya amma mazhaba’r Malikiyya da Shafiiyya sai wadda ta kai shekara daya (1)  Musinnah daga cikin awaki, wadda ta cika shekara daya (1) a Mazhabar Hanafiyya da Malikiyya da Hanabila,shekaru biyu (2) 3 wajen shafiyya.Musinnah daga cikin shanu wanda ya cika shekara biyu(2) a wajen Hannafiya da shafiyya da Hanabila amma a wajen Malikiyya sai shanu sun kai shekara uku (3}. Musinnah daga cikin rakuma ita ce wadda ta cika shekara biyar {5} wannan hukunci duk malamai sun hadu a kansa.8. WA ZAI YANKA DABBAR LAYYA?An so wanda zai Layya ya yanka dabbarsa da kansa sai dai in akwai Ialuri, ya halarci wurin yanka da kansa in haka bai samu ba babu laifi. ’Haka kuma an so a kayar da dabbar ta sashen ta na hagu ta fuskanci alkibla a tabbatar da wukar mai kaifi ce sosai, wanda zai layyar ya ce, Bismillahi Wallahu Akbar. Ya yanka ya ce, Allah ka karba mani da ni da iyalan gidana. Sai su taru a cikin Iadar. Amma ha a yin kudi-kudi a tara ayi Layya. 9. SHIN KO ANA BIYAN MAI AIKIN DABBAR NAMA DA WA NI BANGARE NANAMAN  KO  FATAR?A’a ba a bjyan mai aikin nama da kowane irin bangare na dabbar Layya. Saboda Hadisin Aliyu bin Abi Dalib{RA}wanda Bukhari da Muslim suka ruwaito shi, ya ce, Manzo {SAW}ya umurce ni da in tsaya kan rakumansa na Hadaya da namansu da fatansu da kayan rakuma zuwa ga talakawa, kada in bayar da komi nasu ga wanda ya yi aikin namansu. A nan ke nan sai dai a hiya shi da kudi.

10. YA YA AKE Yl DA NAMAN LAYYANaman Layya anso aka sa shi kashi uku. Kashi guda Iyalin gida da maigida su ci. Kashi guda a yi Sadaka da shi. Kashi guda a yi kyauta da shi. Saboda Hadisin Aisha wanda Bukhari da Muslim suka ruwaito shi, ta ce, Manzo{SAW}ya ce, ku ci, Ku ajiye, ku yi Sadaka. To a nan sai malamai suka ce, ( ya halatta mutum ya yi sadaka da Layyarsa duka, kuma ya Halatta ya cinye duka ya ki ba kowa. Sal dai wanda ya yi haka ya yi asarar Lada maiyawa.SHIN ANA AJIYE NAMAN LAYYA?Eh ana ajiye naman Layya tsawon lokacin da ake so ana amfani da shi, matukar al’ummar da za a bayar da sadakar ko kyauta basa cikin tsanani. Saboda Hadisin Saalamata bin Akawa’i ya ce Manzo (SAW}ya  ce, wanda ya yi Layya cikinku kada ya wayi gari kwana na uku da sauran naman a gidansa. Da shekara ta dawo sai suka ce ya Manzo Allaah za mu aikata kamar yadda muka aikata shekarar da ta wuce. Sai ya ce ku ci, ku ajiye, wancan shekarar mutane suna cikin wahala na so in yi taimako a cikinta, shi ya sa na ce kada a ajiye naman Layya fiye da kwana ukku {Allah ne mafi sani).12. ME NE NE AKA HANA WANDA YA YI  NIYYARYIN LAYYA YI  BAYAN AN GA WATAN  ZULHAJJI?.An hana ma wanda ya yi niyyar yin Layya yanke farce ,da aske gashi daga jikinsa har sai ya yanka Layyarsa .Saboda hadisin Ummu Salamah {RA}wanda muslim ya fitar da shi ta ce, Manzo {SAW}ya ce, idan kun ga Jinjirin watan Zulhaj kuma mutum ya yi niyyar yin Layya to ya kame daga gashin sa da faratansa”. Wannan sunnah ce ta Manzo{SAW}wanda ya yi  ya  samu Iada  wanda baiyi ba ya yi asarar Iada mai yawa.13. WANE AIKIN IBADA NE ALLAH YA Fl  SO RANAR lDIN SALLAR LAYYA?Babu aikin da Allahu {SWA} ya fi so a ranar ldi, irin zubar da Jini na dabbar Layya. Saboda Hadisin Aisha {RA} wanda Tirmizi  ya fitar da shi ta ce, Manzo {SAW}ya ce, Dan’Adam bai aikata wani alki ba ranar Idin Yanka, wanda ya fi soyuwa ga Allah, irin zubar da jinin Layya. Lallai ita za ta zo ranar alkiyama da kahonlnta da gashinta da kofatanta. Jinin Layya zai sauka wurin Allah kafin ya sauka kasa. Anan ana nufin ladarsa daga wurin Allah ta isa ga mai Layya kafin,  jinin ya sauka kasa. Saboda gaugawar ,karbar aikinsa.14. LADA NAWA AKE BAYARWA GA MAI LAYYA IN YA YANKA DABBAR SA?Wanda ya yanka Layya yana samun Lada a kan kowane kwayar gashi na dabbar da ya yanka ko da kuwa dabbar nan ce ta kasar Australia mai gashi kamar auduga sai an bayar da lada a kan kowane kwayar gashi na wannan dabbar in dai an yanka ta da sunan’ Layya.Saboda hadisin sa Manzo {SAW}da aka tambaye shi me ne ne wannan Layya?, ya ce sunnar babanku Ibrahim. Suka ce masa me ke gare mu inmun yi ta?, ya ce, kowane gashi nata za a ba ku lada ,suka ce, gashin sufi fa?, Ya ce kowane gashinta daya za a ba shi lada. {lbn Majah da Tirmizi da Ahmad da Hakim sun fitar da wannan hadisin}.Hakim ya ce Hadisi ne mai dangane inganci.15. SHIN ANA CIN BASH! AYI LAYYAAna iya cin bashl a yi Layya amma idan an san ba za a kuntata ba wajen biyan bashin da kuma bayan an biya bashln. Kamar mai amsar albashi wanda ke jlra a biya shi kuma ga lokaci ya yi bai amsa ba, ko dan kasuwa da ya sayar da kaya za a kawo masa kudi, ko wanda ke da wasu kayan kudi wanda ake nema da ya fltar za a bashi kudi, amma sai ta isa wani gari, da sauran irn wannan.  Wadannan duk za su ci bashi su yi Layya.{Allah ne mafi sani). Sai dai a sani ana yin Layya ne don Allah kuma Allah ba ya azama rai sai abinda take iyawa haka kuma Allah bai sanya maku wannan Addini ya zama tsanani a gare ku ba. Kuma babu tilasci ga addini. Haka kuma wanda ya yi Iayya saboda wani dalili ba saboda Allah ba baya da lada.16. SHIN MAI AIKIN HAJJI YANA YIN LAYYA WATAU YA BAR SAKO GIDA A YANKA MASA?A’a mai aikin Hajji ba ya yin Layya ya bar sako, gida a yanka masa shi yana can Makkah sai  dai ya yi hadayarsa a can, amma nan gida sai  dai ya saya wa iyalan gidansa su yi Layyarsu amma shi ba ya ciki.SANARWA:Wanda ya samu wannan kasida ya samu ya gurza ya raba majama’a. ko kuma ya tura ta kafafen sada zumunta. Na Facebook,Watsaspp,Twittwer da sauransu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *