Spread the love

Daga Aminu Tanimu

Biyo bayan wani guntun bincike da kadan daga cikin ma’aikatan mu suka aiwatar mun fahimci cewa al’umma da dama suna fama da fargabar kada a kwace musu taskarsu ta Facebook wato Account dinda suke amfani dashi a kafar Facebook domin karba da isarda sakonni na sirri dana bayane.
hakan yasa muka yanke shawarar gabatarda wata gajeruwar kasida domin wayarda kan al’umma. Insha Allah duk wanda yabi wadannan matakan to zai tsira daga fadawa cikin irin wannan matsalar, zamu lissafo su kashi-kashi.
Wato idan akace kwace taskar wani domin yin wani amfani da ita batare da umarnin shi ba, to wannan aikin ana kiransa kutse, wadanda ke wannan aikin kuma ana iya a kirasu da “Yan Kutse” ko kuma “‘barayin zati” su kuma ‘barayin zati sun kasu izuwa nau’i-nau’i.
Nau’i na farko: sune wadanda ake kira farfarun ‘yan kutse Nau’i na biyu: sune ake kira koriyar yan kutse Nau’I na uku: su ake kira ba’ka’ken ‘yan kutse
Nau’i na farko sune wadanda suka san duk wani ilimi na yadda ake aikata aikin  kutse amma suna amfani da wannan ilimin nasu ga wasu ma’aikatinne ko kamfunna domin su kare wadannan ma’aikatinne daga fadawa sharrin masu kutse.
Nau’i na biyu sukuma sune wadanda keyin kutse ga wani wuri dake ganin yanada tsaro, sa’annan daga baya su zo su bayarda bayani ga wadanda suka fada hannunsu na yadda za’a warware matsalar.
Nau’i na uku, wadannan sune mafi sharrin mutane daga dukanin nau’o’in ‘yan kutse, domin sune ke bin ko wace irin hanya domin suga cewa sun rabaka da wani abu da kake takama dashi a yanar gizo-gizo. Alal misali, sune ke satar lambobin sirri na banki domin satar kudin mutum, sune ke satar taskokin mutane na kafafen sadarwa domin rabasu dasu, ko ‘bata musu suna. To wadannan mutane sune muke fama dasu anan dandalin sadarwar zamani ta Facebbok.
To, a cikin ko wane fanni daga cikin wadannan kalolin ‘yan kutse akwai ‘Kwararru, akwai ‘yan tsaka-tsaki haka kuma akwai ‘yan koyo.
To Magana ta gaskiya wadanda suka fi damun mu anan najeriya sune “Yan Koyo” wato wadanda suke a matakin farin na koyon harkokin kutse, sune ke tattalin suga sun shiga taskar mutum ta kowace hanya domin suga sun kwace wannan taskar kawai don suji nishadin cewa sun kwace mai taska, sai su ‘dan ji kansu cewa sun fara zama wani abu a fannin kutse.
Bisa tunanin da kuma wani guntun bincike da DANDALIN KIMIYA DA FASAHA suka gudanar tsakankanin wasu masu amfani da manhajar ta Facebook, sun gano cewa akwai wani sake da mutane keyi wanda hakan ke bayarda dama ga kananan ‘yan kutse har su samu dammar ‘kwace musu taska.
Wadannan abubawan sune kamar haka:  •Saka lambar waya a matsayin lambobin sirri (wannan da  yawa mutane nayin haka)  •Barin lambar waya ko Imel a bayyane (Public)  •Taba kowane irin rariyar li’kau (Link) da aka turoma  •Bayarda izini ga wasu shafuka, ko manhajoji da cewa su sami izini na amfani da bayanan taskar ka  •Amsa gayyatar abokantaka ta wasu mutane wadanda baka sani ba  •Shiga manhajar Facebook da na’urori daban-daban batareda ficewa ba, bayan kammala bukata  •Shiga dandalin Facebook da na’urar Tashar lilo (Internet Café) kuma wa’adin da ka siya yakare batareda ka fice ba. dsr.
Bayan haka, munyi nazari akan wasu matakai daya kamata mutum ya dauka domin ganin cewa ya kare wannan taskar tashi, sune kamar haka:
 Saka Lambobin sirri masu tsauri (Strong Password) wadanda basu danganci suna, lambar waya, ko ranar haihuwa ba.  Mutum ya dinga canza lambobin sirri na taskarshi lokaci-zuwa-lokaci (wata-wata)  Gujewa shiga ko wane irin Rariyar likau (Link) da aka turo maka  Kada ka bayarda izini ga wasu manhajoji ko shafuka izinin amfani da bayanan taskarka.(Idan ka bayar ka dau matakin tsayarwa)  Ka duba duka na’urorin da taskarka ta Facebook ke akai  Mutum ya saka matakin tsaro na tantance Lambobin sirri na biyu (two-step authentication)
Domin sanin yadda zaka dau wadannan matakan:
 Yadda ake saka Lambobin sirri masu tsauri, anaso ka saka Harufa tsakanin Manya da ‘kanana (A-Z) da (a-z) sai “Characters (.,!@#$%^&|*(){}[]’+_-\dsr)”sai lambobi 0-9 to idan lambobin sirri suka kumshi duka wadannan zaiyi wuya a iya tunanin su.  Ana canza lambobin sirri dai-dai yadda mutum bazai wahala ba, sati-sati, wata-wata, ko duk bayan wata uku (in son samu ne kada ya wuce wata uku ba tareda an canza ba)  Wannan matakin mai sauki ne kawai idan wani ya turoma da wani adireshi wanda baka gane yanda yake ba, to kada ka taba, ka barmasa abinsa.  Akwai wasu Shafukan yanar gizo-gizo da suke baka damar cewa kana iya hada taskarka ta Facebook da shafinsu domin su buda maka tasu taskar ba tareda kasa suna ko lambobin sirri ba, kada kayi, kaje ka cike bayanan da suke da bukata dasu domin budema tasu taskar idan har kanada bukata dasu. Idan kuma kariga ka bayarda wannan izinin, ga yadda zaka soke;  Ka shiga Facebook → Settings and Privacy → Settings → Apps and Websites → Logged in with Facebook → Sai ka taba duk wanda bakada bukata dashi daga nan sai ka taba maballin “REMOVE” ka bayarda amincewa shikenan sun rasa wannan izinin.  Wannan matakin yanada kyau kwarai da gaske, domin tanan ne kawai zaka gane duk inda aka shiga cikin taskar ka, zakaga bayanin na’urar da akayi amfani da ita domin shiga, idan kaga na’urar da bakada ita to daga nan zaka iya fitarda taskarka daga waccan na’urar kuma kana iya kai korafi akan wanan, domin daukar wannan matakin: Ka shiga Facebook → Settings and Privacy → Settings → Security and Login → where you’re logged in → See more (Idan akwai wata na’ura dabaka amince ma ba, sai ka ta’ba ma’ballin dake gehen damanta sai kasa “Log Out” Shikenan.  A halin yanzu shine babban matakin tsaro da ake amfani dashi domin ganin an kare taska bakin gwargwado, domin saka wannan tsaron Ka shiga Facebook → Settings and Privacy → Settings → Security and Login → Setting Up Extra Security → Use two-factor authentication → Ka zabi “Text Message” → Sai ka saka Lambar wayar da za’a dinga turoma da sa’ko → Za’a turoma lambobin sirri masu amfani sau daya(OTP) guda shida (6) sai ka saka su dan akwatin da Facebook ya tanada → Sai ka bayarda amincewarka. Shikenan baza’a taba shiga taskarka ba, batareda an turo Lambobin sirri guda shida ko biyar a wannan layin naka ba.  dole sai an turosu, an dauke ansa sannan za’a samu damar shiga wannan taskar. Allah ya datar damu.
Aminu Tanimu ArzikaShugaban Dandalin Kimiya da Fasaha03rd Aprilu, 2019

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *