Spread the love

Bello Sambo Bazza

    A wannan karni na ishirin da daya, abin da Hausawa ke fadi ne ga koshi ga kwanan yunwa ke tattare da wannan al’umma,  duk da kasancewar hanyoyin karatu da makarantu sun karu ainun,  sai dai a ko yaushe cikin zukatun wasu iyaye da su kansu ‘yan matan su na ganin cewa, shin su ci gaba da karatunsu kafin aure ko  su jinkirta karatun har bayan aure?

  A saboda da wannan sar}a}iyar, mujallar “Managarciya” ta shiga gari domin jin ra’ayin jama’a.

   Malama Zainab Harisu,  ta ce tafi son sai ta yi karatu sosai, kafin aure ya biyo baya, akan wasu matsaloli da ta fahimta.  Wani lokaci sai anyi alkawari da mutum na cewa zai bar matar sa ta ci gaba da karatu,  amma da zarar matar ta shiga gidan sa, sai kawai ya sha mur yace shi sam ba da shi aka yi wannan magana ba.

   Ta ci gaba da cewar, irin matsalar juna biyu wani lokaci ko kina kan karatun,  saboda laulayin ciki sai karatun ya lalace, har ma in ya kasance babu doguwar kulawa daga sashen uwayen yarinyar ko ita kanta ko mijin, shi ke nan karatun ya bi iska har dai in babu hali sosai a tare da su.

  Hajaru Isma’ila ta ce ‘}ila saboda yanayin tatalin arziki da mu ke ciki, samarin yanzu ba su son macen da ba ta yi karatu ba, saboda mace mai ilmi a harkar lafiya ko malanta da sauransu, sun kan taimaka wani lokaci a rufa wa juna asiri. Haka kuma sun fi iya abinci da shirya yara da kwalliya.’ A cewar Hajaru wadda take ]aliba ce a kwalejin ilmi ta Shehu Shagari dake Sakkwato.

   Wata ]aliba wadda ta ke kusa da kammala karatun ta na sakandare da ta nemi a sakaya sunan ta cewa ta yi “Ba zan so in yi aure kafin kamala karatuna ba, domin na fahimci mafi yawan yayuna  sun yi aure ne bayan sun kammala karatunsu na gaba da sakandare, kuma wannan bai hana su; su auri mazan da suke bu}atar su aura ba” a kalamanta ga Managarciya.

     Ta kuma }ara da cewar,  ‘na fahimci dukkanin su (yayuna)  suna zaune da mazajen su cikin kwanciyar hankali da kulawa, wanda hakan yaba su damar ]aukar wani ~angare na wasu harkokin gida da ]an abin da suke samu daga albashin su” in ji ta.

    Balkisu Bello na da ra’ayin cewa,  ta yi karatu bayan ta yi aure, a matsayin ta na ‘ya mace zai fi dacewa, saboda ta fahimci yin aure kafin karatu na sanya  mace ta zama mai natsuwa.

  “Mace za ta  kare kanta, sannan ta san karatun ne kawai a gabanta, ba tare da fargabar bayan karatun waye za ta aura ba.In mace ta jajirce ta mi}e ta ta}aita yawan kallon fina-finai da  tashoshin duniya da barci marar kan gado a na iya yin nasara.

 “Mata da dama a wannan }asa, da su ka ri}e muhimman mu}amai a gwamnati,  mafi yawa daga cikin su tun digirin farko har ya zuwa zama shaihun malaman Jami’a (professors) a gidajen mazajensu suka yi karatun, kuma a cikin aljihun mazajen su ne.” In ji malama Balkisu.

   Managarciya ba ta yi }asa a guiwa ba ta nemi jin ta bakin maza don tofa albarkacin bakin su. Malam Bashiru Sahabi na da ra’ayin cewa, tun da addininmu bai hana mata neman ilmi ba a ko’ina yana da kyau mata su yi karatu.

  ‘Duk da ya ke ni magidanci ne, amma gaskiya idan zan sake aure zan  bar matata ta yi karatu, in kuma ta na kan yin karatun ne zan barta ta kamala.

[aukar nauyin karatun na sanya matan wannan zamani zaman aure, ta ri}a girmama
ka sa~anin ka ha]

u da ita bayan ta kammala karatun ta.

   Malam Adamu Shehu, a ganin sa ko sun yi karatun sun fara aiki, ba wani taimako da ke shigowa a gidan mazajensu, in ba ka yi sa’a ba karatun na zama barazana a tafiyar da harkokin ka na waje, don haka shi bai gamsu matarsa ta yi karatu ba.

  Malam Mansur Yusuf ya ce, “Yana son mace mai yin karatu a cikin gidansa, amma  akwai wani hanzari ba gudu ba, shin  bayan karatun ana tsammanin ta sami aiki, bayan ta samu, sai ka ga ba wani taimakon da ke shiga tsakanin ka da ita”. 

Yana da kyau, duk macen da za ta yi karatun gaba da sakandare bayan ta yi aure,  ta kasance matar da ba ta da lalaci, tana aiki tu}uru, yadda karatun zai kasance bai damuwar  mijin. Amma a duk lokacin da  ayukkan gida suna fa]uwa saboda karatu, to dole ne ka ga mijin na }o}arin ganin ya bi hanyoyi na hana karatun. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *