Spread the love
DAKTA AISHA BALARABE BAWA

Daga Sadiya Attahiru

Dakta Aisha Bawa mace ta farko a matsayin Mataimakiyar shugabar {ungiyar Malamai ta jami’ar Usman Danfodiyo da ke jihar Sakkwato, ]aya daga cikin jagorori a fannin  ilmin tarihi na Nijeriya, tana cikn mata }alilan da suka yi kar~ar sakamakon za~en 2015, ta yi tafiye-tafiye kan harkar ilmi a }as ashen Turai. Mace mai gaskiya da ri}on Amana da son cigaban al’ummarta musamman mata, tana aiki tutu}uru don samar da al’umma ta gari.

Dakta Aisha a zantawarta da Managarciya ta yi magana kan mu}amin da take saman shi a yanzu  “Lalle akwai gwagwarmaya a shugabancin }ungiyar malamai na jami’a  a hannun mace abu ne da ake kallo sabo a lokacin da ake bani mu}amin, kasancewa a Arewacin Nijeriya ba a cika ganin mata suna gwagwarmaya da maza a harkar shugabancin kungiya ba, musamman wanan da ke fafutikar nemawa malamai ha}}insu da tabbatar  da ingantuwar ilmi a }asa baki ]aya.  Ina da ra’ayi ga abin da ya shafi kwatanta gaskiya da nemawa mai ha}}i ha}}insa musamman talakawa da mata,  haka ya sanya na yi aiki da }ungiyoyi masu zaman kansu”.

“A wannan yanki namu naga kamar mata ba su bayar da muhimmanci  a wajen gwagwarmaya domin rashin ba su dama, dubi siyasar Nijeriya za ka ga ba su da yawa,  an saka al’ada da amfani da addini a danniyar ta  maza, ba su baiwa mata ha}}insu a wajen gudanar da mulki yana cikin abin da ke }ara kawo cikas ga cigaban mata har a jami’o’i amma yanzu abin ya fara gushewa har an samu mace shugabar jami’ar Jigawa.” A cewar Dakta Aisha.

Da ta koma kan abin da ya }arfafata ta ce  “Na samu goyon baya don ita mace duk abin da za ta yi in ba ta samu ha]in kan maza ba, sun ba ta dama to abun ba zai yi wu ba. A harkar }ungiya Farfesa Sule Kano ya }arfafani ya bani dama aka sanni da rawar da nake iya  takawa a }asa na yi aikace-aikace har shirya za~e da taruka, kasancewar hakan ne ya sanya na dawo gida yankina don muna da gi~in mata a shugabannin }ungiya, sai aka nemeni na zama mataimakiyar ciyaman na aminta, na yi haka ne don mata su tabbatar suna iyawa ba da ta su gudunmuwa, kuma sai   ri}a janyo mata ina  sanya su cikin kwamitoci in za mu yi horaswa na NDC da wasu wuraren, akwai wani horaswa da ake  bu}atar mutum 50 na sanya mata 15 a ciki, a yanzu ko bani nan na tabbata an samu mata da  za su iya cigaba da in da na tsaya. Abu ne da muke bu}ata in mace ta samu ta jawo ‘yan uwanta su samu, mu bar adawa da jin haushin junanmu.” In ji ta.

Wa}iliyarmu ta nemi ta }ara bayani kan }warin guiwa da jajircewar mata, don har yau ba’a ganin mata na iya bayar da gudunmuwa a waje.

“Kamar yadda na fa]a a farko abu ne da ya shiga cikin jinin mutanenmu ba a arewa ka]ai ba, abu ne da ya mamaye duniya koyaushe namiji na ganin shi ne gaba mace tana }asa don mi za ta yi gwagwarmaya da namiji duk da matan ne, ke da kashi 50 na mutanen duniya kuma suna iya kawo cigaba ta ~angarensu, ja bayansu na kawo cikas a tattalin arzikin }asa da ilmi da mulki, aba su dama ba yana nufin mace ta zama kamar namiji ba, ko ta yi kafa]a da shi, mazan sun }i yarda su aminta su baiwa mace damar da addini ya ba ta, a neman ilmi da bayar da gudunmuwa. Ana sanya addini da al’ada wajen kange su ba su samun isasshen ilmi da arziki da kar~uwa, an sa musu tsoro da rauni sun yarda ba su iyawa, su matan sun }i la’akari duk abin da aka ce ba su iyawa sun zo sun yi shi sun wuce wurin.” Kalaman Dakta kenan.

 Dakta Aisha Bawa ‘yar asalin jihar Kebbi ce da ta yi dukkan karatunta a Sakkwato, ta ce  “Mijina ya bani gyon baya ]ari bisa ]ari, don yasan abin da nake yi abu ne na taimakon al’umma.”

“Abaiwa mata ilmi su fahimci }alubalen da ke gabansu su kuma san duk abin da za su yi }asa suke ga maza, ba wata mace da ta zama wani abu ba mijinta ne ya taimaka mata ba, mata uwaye ne masu tausayi  samunsu alheri ne a gida, a ri}a ]aga masu ana janyo su a jiki, ga abin da ya shafi aikinsu na cigaban al’umma. Mace ba baiwa ba ce, abokiyar zama da shawara ce, musulunci bai yarda maza su tauye ha}}in matansu ba, ya ba ta dama ta mallaki ku]in kanta ta hanyar yin sana’o’in da shari’a ta aminta da su, in mace ta zama tana da nata zai }ara taimakon aurenta da iyalinta.” Dakta Aisha kenan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *