Ƙasar Saudiya Ta Yi Matsayar Ba Za Ta Hana Aikin Umara Ba Duk Da Dawowar Korona

Ƙasar Saudiya Ta Yi Matsayar Ba Za Ta Hana Aikin Umara Ba Duk Da Dawowar Korona
Ma'aikatar Hajji da Ummara a Saudi Arebiya ta musanta jita-jitar da ake bazawa  wai za a dakatar da aikin Ummara sakamakon ƙaruwar annobar korona, bayan zuwan sabon nau'in cutar mai suna Omicron.
Wata majiya a ma'aikatar ta shaidawa shafin yanar gizo na Haramain Sharifain cewa Maikatar ba ta da niyyar dakatar da umrar da ake yi,  amma dai ta na kira ga baƙi da alhazan Ummara da su kiyaye da matakan kariya da mahukunta su ka ɓullo da su.
A kwanannan me dai Babban Ofishin Kula da Masallatan Harami Guda Biyu ya dawo da tsarin bada tazara da juna da kuma sanya takunkumin fuska a Masallatan biyu masu tsarki bayan ƙaruwar cutar ta koron.
"Mu na kira ga duk wani alhaji da masu ziyara da su kiyaye da matakan kariya na bada tazara da juna da sanya takunkumin fuska. Hakan zai tabbatar mana da kariyar kan mu da ta yan'uwa," in ji Limamin Masallacin Harami na Makka,  Sheikh Yasir Al Dossary.
Wannan matakin zai faranta musulman duniya musamman waɗanda suka yi niyar zuwa umra da masu shakkun hana su zuwa aikin hajjin wannan shekara.