Ɗan Wasan Hausa Sani Garba S.K  Ya Rasu

Ɗan Wasan Hausa Sani Garba S.K  Ya Rasu
SK

Allah Ya yi wa fitaccen ɗan wasan fina-finan Hausa Sani Garba SK rasuwa a yau Laraba a birnin Kano, bayan ya sha fama da rashin lafiya

Wani fitaccen furodusa Abdul M Amart Mai Kwashewa ne ya tabbatar wa da BBC rasuwar ɗan wasan.

Marigayin ya rasu ne a Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase da ke Nasarawa a ranar Laraba da yamma.

"Sani SK ya kai kusan shekara uku yana jinya a tsattsaye, amma rashin lafiyar ta taso masa sosai ne a baya-bayan inda ya shafe mako biyar yana jinya a asibitin," in ji Amart.

A kwanan baya margayin ya musanya batun rasuwarsa da kansa sai yau ga shi  Allah ya karɓi rayuwarsa.

'Yan wasan Hausa za su yi jiname rashin ɗan uwansu a wannan lokacin da suke buƙatar irinsa a cikinsu.